FRSC ta horar da ZAROTA kan harkokin zirga-zirgar ababen hawa tare da yimasu gargadi game da cin zarafin jama'a a Zamfara
Daga Aliyu Buhari Gusau Hukumar Kula da Tsaron Hanya ta Tarayya (FRSC) ta gudanar da horo ga hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Zamfara (ZAROTA) kan harkokin zirga-zirga, tare da yimasu gargadi game da cin zarafin jama'a a jihar. An gudanar da horon ne a zauren taro na kungiyar NURTW da ke kan hanyar 'Bye-pass' a Gusau, babban birnin jihar. Kwamandan hukumar FRSC na jihar, Aliyu Ma'aji, ya bayyana cewa an shirya horon ne domin fadakar da jami'an ZAROTA kan dokoki da ka'idojin da ke tafiyar da harkokin zirga-zirgar ababen hawa. Aliyu Ma'aji ya jaddada cewa, ba a yarda jami'an ZAROTA su rika tsoratarwa, kunyatawa, ko bata sunan kowa ba. Ya kuma yaba wa Kwamandan ZAROTA bisa kokarinsa na inganta harkokin hukumar. A nasa jawabin, Kwamandan ZAROTA, Muhammad Bello Musa, ya yabawa 'yan sanda, hukumar Civil Defence, da kuma DSS bisa goyon bayan da suke bai wa ZAROTA. Ya bayyana cewa akwai kararrakin da suka shafi ZAROTA guda 48 a kotu, i...