AN KADDAMAR DA SHUGABANIN ZABARKANO A JIHAR ZAMFARA
Daga Haruna Muhd Gusau
An kaddamar da shugabanin kungiyar Zabarmawa na jahar Zamfara, ZABARKANO.
Waddanda aka kaddamar a matsayin shugabanin sune,
Alhaji Hussaini Tawai, a matsayin shugaba, Alhaji mustapha Ismail kwando, mataimakin shugaba 1, Alhaji Usman saidu Dausayi, mataimakin shugaba 2, Alhaji Gado Abdullahi Noma polo, Ex officio, yayin da aka zabi Shehu Abdullahi Bankanu a matsayin babban sakatare.
Sauran shugabanin sun hada da ; Alhaji Abdullahi Na Gusau, Ma'aji, Alhaji Ibrahim , sakataren kudi, Kabiru Umar, sakataren tsare-tsare, Muhd Ahmad, Mai binciken kudi, Alpha yakubu zumunchi, sakataren walwala, sai Kuma aka zabi Alhaji Murtala General a matsayin Mai watsa labarai na kungiyar waton( PRO)
An dai kaddamar da shugabanin a Maryam Multi purpose hall a Tudun wada Gusau. Kuma National Deputy president na kasa shine ya kaddamar da shugabanin, Alhaji Ibrahim Ahmad Gusau, da yake jawabi yayin kaddamar da shugabanin yace wannan kungiyar waton zabarkano tayi fice Tana da rasa a wajen kasa shen duniya da suka hada, France, Niger, Ghana, Barkina faso,da dai sauransu.
Dalilin kafa wannan kungiyar shine a inganta ya ran zabarmawa waton zabarkano a fadin duniya domin hada kawunan su wuri daya.
Daya daga cikin tsaffafin shugabanin da suka aje muka mansu bayan sun Rika na wani Dan lokaci a Wanda Kuma shugane a National body, waton, Alhaji Gado Abdullahi Noma polo, Shima ya tofa albarkacin bakinsa yace kam bai Raina asalinsa duk inda ya tsin ci kan sa dole yayi bugun gaba da yaran zabarmawa waton zabarkano, saboda shine asalin sa.
Shima dai sabon shugaban na zabarkano, Alhaji Hussaini Tawai, ya godewa membobin kungiyar da suka zabe shi a matsayin chairman na zabarkano, ya kuma yi alkawalin hada kawunan yayan kungiyar wuri daya tare kudirin bullo da hanyoyin taimakawa marayu da marasa galihu domin samun damar yin karatu domin su zama wani Abu gobe a cikin alummah.
Daga karshe ya umurci dukkanin yanyan kungiyar da su sayi form a #200 a cika wannan shi zai baka damar kazama cikkaken Dan kungiyar zabarkano
Itama dai National women leader ta kasa Hajiya Talatu Ahmad Gusau, a nata jawabi tayi Kira ga mata da bada hadin Kai wajen inganta yaran zabarmawa da cigabansa, ta nuna jin dadinta irin yadda taga dandazon mata sun halaci waton wannan kadamar wa ana fatan wannan ya daure a cikin jahar zamfara da kasa baki daya.
Comments
Post a Comment