Hukumar zabe ta kasa ta raba muhimman kayan zabe na gwamna dana ‘Yan majalisun jiha ga kananan hukumomi a jihar Kebbi
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta raba muhimman kayayyakin zabe na gwamna da na majalisar dokokin jiha a jihar Kebbi.
Da yake zantawa da manema labarai yayin rabon kayayyakin a ofishin babban bankin Najeriya reshen Birnin kebbi, kwamishinan zabe na jihar, Ahmed Bello Mahmud ya bayyana cewa sun isa babban bankin ne domin ganin duk wasu muhimman kayayyakin da suka hada da Katin zabe da takardar sakamako da kuma tabbatar da cikar su sannan a tura su ga kananan hukumomin jihar.
Ya bayyana cewa, za a fara rabon muhimman kayan zabe ne daga mazabar Kebbi-South sai kuma gundumar Kebbi ta Arewa da kuma Kebbi ta tsakiya a karshe saboda kusanci.
"Za mu sake yin atisayen horas da ma'aikatan mu na Ad-hoc domin mu yi fatali da wasu kalubalen da aka shaida a lokacin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya” inji Kwamishina.
Kwamishina Ya kuma bayyana cewa, an riga an tura duk wasu kayayyakin da ba su da muhimmanci ga kananan hukumomi tun bayan zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya, yana mai bayyana tsarin tsaro da kayan aiki a matsayin abin burgewa.
"Wani bangare na yarjejeniyar kuma zan sanya hannu kan dukkan fom din saboda tsaro” Kwamishina yatabbatar da haka.
Ya godewa sojoji da hukumomin tsaro bisa jajircewarsu na ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a jihar
Comments
Post a Comment