Kungiyar 'yanjarida takasa reshen jaridar dab'i ( legacy) taraba kayan abincin azumi ga mambobinta.
Daga Aliyu Buhari Gusau
Kungiyar 'Yan Jaridu takasa reshen jaridar dab'i (legacy). taraba abincin azumi ga mambobinta.
Da yake jawabi a lokacin rabon abincin azumi, shugaban kungiyar Kwamared Bilyaminu Muhammad Gusau, ya bayyana cewa, hakan na daga cikin kokarinsa na ganin an samu saukin rayuwa ga mambobinshi. yana mai alkawarin cewa za a ci gaba da gudanar da irin wannan.
Kwamared Bilyaminu Muhammad ya ci gaba da cewa, kayan abincin da akaraba kowane mutum guda zaisamu kwalin taliya, yabukaci mambobinshi dasuyi amfani da abinci kamar yadda yaddaci.
Kwamared Bilyaminu ya kuma yi alkawarin samar da abubuwan hidimar sallah ga mambobinshi.
Shugaban kungiyar ya yayabawa mambobinsa bisa goyon baya da hadin kai da sukabashi, inda ya yi kira gare su da suci gaba da yin hakan.
Comments
Post a Comment