Daga Aliyu Buhari Gusau
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Kolo Yusuf, ya gana da shugabannin hukumomin tsaro, inda suka tattauna sosai kan yadda ake gudanar da harkokin tsaro a zaben gwamna da 'Yan majalisar dokokin jihar a ranar 18 ga watan Maris.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Kakakin Rundunar SP Muhammad Shehu ya sanyawa hannu kuma ya mika wa Jaridar gaskiya.
A cewar sanarwar, Kwamishinan 'Yan sandan kolo Yusuf da takwarorinsa sun kuduri aniyar inganta tare da dorewar hadin gwiwar aiki don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar ta yadda za a samar da yanayi mai kyau na gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci da kwanciyar hankali.
Kwamishinan ‘yan sandan yabada tabbacin bada tsaro kafin lokacin zabe da kuma bayan lokutan zabe, ya bukaci jama’a da su kasance masu bin doka da oda tare da gargadin masu tayar da kayar baya da su nisanci duk wani abu da zai iya kawo cikas ga jama’a.
Comments
Post a Comment