Daga Aliyu Buhari Gusau
Kwamandan Rundunar Tsaro ta Cibil Defence na Jihar Zamfara Muhammad Bello Muazu, yajahankalin jami’an sa dasu tsaya tsaka-Tsakkiya a ayyukansu a lokacin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Ikor Oche SC ya sanya wa hannu yabaiwa jaridar gaskiya.
A cewar sanarwar, Kwamandan Muhammad Bello Muazu ya bayyana hakanne a yayin da yake jawabi ga jami’an tsaro a hedikwatar jihar Gusau, “Rundunar ta yi amfani da dukkanin bangarori na rundunar domin tabbatar da an samu ‘yanci, da adalci”
"A bisa ga dokar zabe, rundunar ta tabbatar da cewa an tura isassun ma'aikata tare da sauran hukumomin 'yan uwa domin dakile duk wata barazana ga masu zabe da jami'an da ke gudanar da zaben" MB Muazu yace haka
kwamandan MB Muazu ya bukaci dukkan jami’an da aka tura domin gudanar da zaben su kasance masu himma da tsaka-tsakkiya da kuma saka baki wajen gudanar da ayyukansu a lokutan zabe da kuma bayan zabe.
MB Muazu ya nanata kudurin hukumar na taimakawa hukumar kula da kare rayuka da dukiyoyi a jihar a lokacin zabe.
kwamandan ya umarci al’ummar jihar Zamfara nagari da kada su damu domin rundunar ta samar da isasshen tsaro a lokacin zabe da kuma bayan zabe
Comments
Post a Comment