AN NEMI ZABBABIN YAN MAJALISAR WAKILAI TA TARARYA DASU GOYAMA DR, SANI JAJI BAYA DOMIN YA SHUGABANCI MAJALISAR




Alhaji Hamza Maibulawus

FROM HARUNA MUHD GUSAU

Shaharraren  dan kasuwanan na jahar Zamfara,  Alhaji Hamza Mai Bulawus  ya yi Kira ga dukkanin zabbabun yan majalisar wakilai ta Nigeria su 360 dasu goyawa Dr, Sani Jaji baya ya jagorance su a matsayin shugaban zauren majalisar akaro na 10th domin cigaban al-ummar kasa baki daya.

Alhaji Hamza Mai Bulawus ya yi wannan Kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a babban birnin jahar Zamfara a garin Gusau.

A cewar dan kasuwar, zaben Hon Aminu Sani jaji a matsayin Wanda zai wakilci zauren majalisar wakilai ta Nigeria shine zai  Dore ga roman demokaradiyar kasar.

Haka zalika Dan kasuwar ya shawarci dukanin alummar jahar zamfara da su tashi tsaye wajen yiwa sabon zabbaben Dan majalisar wakilai addu'oi domin samun wannan matsayi, wannan zai taimaka wajen cigaban al ummar jahar zamfara baki daya.

Sannan kuma Dan kasuwar yayi tsokaci ga sabon zabbaben Gwamna jahar zamfara Dr, Dauda Lawan Dare da ya yi kokarin fito da hanyoyin da dubaru da zasu taimakawa al-ummar jahar zamfara domin dorewar demokaradiyar a jahar

Ya Kara da cewa wannan yazamo kalubbale ga zabbaben Gwamnan idon akayi lakari da yadda jama'a suka fito konsu da kwarkwatarsu a 18/3/ 2023 suka zabeshi kyauta a bisa ga kyautata zaton cewa zai yi adalci tare da kawo hanyoyin cigaba a jahar.

Ya Kuma roki al - ummar jahar zamfara dasu cigaba da yimasa addu'a Allah ya bashi ikon kyautatawa al - ummar jahar ta hanyar kawo ayukan alheri da Kuma cigaban al - ummar.

Comments

Popular posts from this blog

Permanent Secretaries' Forum Elects New Executives in Zamfara

Zamfara NSCDC Hosts Acting Provost FCET Gusau

Insecurity: Zamfara hospitals surfer brain drain - Doctor call rescue