MATSALAR KARANCIN RUWAN GUSAU ZATA ZAMA TARIHI - ENG BUHARI SALISU DOSARA MD ZAMFARA WATER BOARD


Eng Buhari Salihu Dosara


FROM HARUNA MUHD GUSAU

An yi Kira ga alummar  cikin garin Gusau da kewaye dasu Kara hakuri dangane da matsalar karancin ruwan Sha da ta addabe su.

Wannan Kiran  ya fitone daga bakin shugaban hukumar bada Ruwansha ta Zamfara, Eng Buhari Salihu Dosara  a lokacin da yake ganawa da manema labaru a ofishinsa.

Eng Buhari Salihu Dosara yace matsala ta faru ne sanadiyar karanci wutar lantarki dake addabar jahar  musamman babban birnin jahar.

Ya Kuma ba al-ummar jahar hakuri in sha Allah injiniyoyinsu suna nan su na bakin kokarin don tabbatar da cewa matsalar tazamo  tarihi a cikin jihar baki daya.

Ya Kuma Kara da cewa ma'aikatan gidan ruwa suna iya yin su domin tabbatar da cewa ruwan Sha sun yawaita 24 hour ga  al-ummar jahar Amma saboda wasu matsalolin  musamman abin da ya shafi na urorin bada ruwan Shan akasarin sun jima suna Aiki fiye da shekaru 30 ana amfani dasu.

 Manajan Wanda yayi fatan alheri ga Mai Daraja zabbaben Gwamnan Dr Dauda Lawan Dare 

 Ya Kuma shawarci alummar jahar Zamfara dasu cigaba da i addu'oi indon aka rantsa dashi 29 may 2023 ya zama alheri a jahar baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Permanent Secretaries' Forum Elects New Executives in Zamfara

Zamfara NSCDC Hosts Acting Provost FCET Gusau

Insecurity: Zamfara hospitals surfer brain drain - Doctor call rescue