Ramadan : Kungiyar agaji ta JIBWIS ta raba kayan sawa ga marayu 205 a Zamfara
Daga Aliyu Buhari Gusau
Kungiyar agaji ta yankin Sabon gari dake karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara ta raba kayan sawa ga marayu 205 a jahar.
Da yake jawabi a lokacin rabon kayan tallafin a Gusau, Shugaban Agajin na sabon gari Malan Suleiman Abubakar Maidabo ya ce sun dauki wannan matakin ne don taimakawa marayu a lokacin bukukuwan Sallah mai zuwa a jahar.
Abubakar Maidabo ya ci gaba da cewa sun kuma raba kayan abinci ga marayu.
Ya jaddada cewa shekaru takwas ke nan kungiyar tana rabon kayan abinci da kayan sawa wayanda daidaikun mutane ke bayarwa, ga Maison bada gudummuwa ga lambar asusun ajiya don taimakawa.
Bank : Jaiz
Account Name : First aid group (jibwis) sabon gari detachment orphanage Gusau
Account no : 0007970962
Phone numbers : 08037547105, 08067312018, 08069582870
Ya yabawa duk wadanda suka bayar da gudumawa ta kowace hanya don samun nasarar rabon kayan, yayi kira garesu dasu cigabada taimakawa.
A nasa jawabin Malan Makiyu Suleiman ya nuna farin cikinsa da rabon tallafin, ya kara da cewa taimakon marayu wata hanya ce ta kusanci ga Ubangiji.
Ya yi kira ga ’yan siyasa da masu hannu da shuni da su yi koyi da irin halin kirki na kungiyar agaji ta sabon gari, ya kuma yi addu’ar Allah ya saka musu da alheri.
A nasa jawabin shugaban kungiyar ta karamar hukumar Gusau, Malan Yusuf Hussaini, ya bayyana rabon tallafin a matsayin maraba da ci gaban marayu, ya kuma yi kira ga yan agajin sabon gari dasu fadada shirin.
A nasu jawabai Malan Anas da Malan Abudurasheed Yusuf Maikwano sunyi maraba da duk wadanda suka halarci shirin, sun godewa duk wadanda suka halarci taron.
Comments
Post a Comment