HUKUMAR ALHAIZAI TA ZAMFARA TA KWASHE MANIYYATA 3,100 ZUWA SAUDIYYA
Daga Haruna Muhammad
Hukumar aikin hajji ta jahar Zamfara tasamu nasarar kwashe dukkanin maniyyatan jahar su 3,100 zuwa kasa mai tsarki batare da wata matsala ba.
Mukkadashin shugaban hukumar alhazzai na jahar, Alhaji Anas shuaibu Mafara a lokacin da yake zantawa da manema labarai daga kaffafen wasa labarai daban daban a office dinsa dake hukumar a garin Gusau ya tabbatar da haka.
Alhaji Anas Shuaibu Mafara wanda shine babban sakatare na hukumar alhazzai ta jaha, ya kara da cewa tunda aka fara daukar maniyyatan ba'a tsaya ba har zuwa jirgi na 8 kuma na karshe. Alhaizan karamar hukumar Gusau su 200 cif su ne sawu na karshe zuwa kasa mai tsarki.
Shugaban hukumar alhaizai yace wannan wata babbar nasara ce da hukumar ta sa mu cikin sati guda aka kwashe dukkanin alhazai aikin bana na shekara 2023 su 3,100 ba tare da kowace irin matsala ba.
Anas Shuaibu Mafara ya kuma tabbatar da cewa hukumar tasu tayi tsari Mai kyau tare da kyakyawar kulawa akan alhazzan don ganin cewa sun gudanar da aikin Hajj cikin Jin dadi a can kasa mai tsarki.
Shugaban yace ganin cewa babu Amirul Hajj a wannan shekarar 2023, sai jagororin hukumar da Directocin ta zatayi iyayin ta don tabbatar da nasara Aikin alhaizai.Ya Kuma ce tsarin da akayi wajen Daukar alhaizai in Sha Allah wajen kwasosu a kasa Mai TSALKI hukumar tayi tana di tare da sun dawo gida zamfara cikin lokaci bayan an Kamala Aikin hajjin.
Lokacin da yake zantawa da kaffafen wasa labarai an tambaye shi ko sun kula da Alhaizai da suka bada kudin su tun farko Deposit yace lai kimanin maniyyatan 2000 suka bada ajiyar kudinsu tun 2020 kuma an basu fiye da wata guda 1 wston one month don su cika kudin Amma mutum 500 kwai suka kawo kudin su cikin lokaci ita Kuma hukumar Aikin hajji ta kasa da taba date line to bafa jira zata yi ya zama wajibi acika gurabensu da wasu maniyyatan. Daga karshe shugaban hukumar alhaizai ta jahar zamfara ya godewa dukkanin kaffafen wasa labarai saboda gagarumar gudumawar da suka bada wajen kwashe Alhaizai zuwa kasa Mai TSALKI.
Comments
Post a Comment