SHUGABAN KWAMMITIN JIN DADIN ALHAIZAI NA JAHAR ZAMFARA YA KUDURCI GANIN ALHAZZAN JAHAR SUN CI NASARAR AIKIN HAJIN BANA
![]() |
Shugaban kwamitin kula da jin da din alhazzan jihar Zamfara Alhaji Musa Mallaha |
FROM HARUNA MUHD GUSAU
Shugaban kwamitin kula da Jin dadin alhazan jahar Zamfara, Alhaji Musa Mallaha(Talban Gusau) ya Jaddada kudurinsa na ganin cewa alhazan wannan shekara ta 2023 sun gudanar da aikin su cikin jindadi da nasara.
Shugaban kwammitin wanda ba da jimawa ba Dauda Lawal, Gwamnan Zamfara ya nada domin ya jagoranci maniyyatan bana na wannan jahar a kasa mai TSALKI.
Musa Mallaha wanda ya zanta da manema labarai da ban da ban a lokacin da ya kammala taron farko da ma'aikatan hukumar a ofishin ta dake kusa ma'aikatar kudi ta jaha,
ya kuma ce dalilin wannan taron shine domin su samu hadin kan ma'aikatan hukumar don su hada hannu wajen ganin anyi kyakyawar tsare ga maniyyatan jahar a kasar Saudiya.
Shugaban kwammitin jin dadi alhaizan na jahar yace hakan kadai zai taimaka wajen magance matsalolin nan da ce a lokacin da ake gudanar da aikin haij a kasar Saudiya mai tsalki.
Talban Gusau wanda yace aikin hajji ba bakon abubane a wajensa ganin ya kwashe kusan shekara 20 yana Aikin hajji wannan zai taimaka masa wajen bada tasa gudun mawa ga alhaizan jahar.
Shugaban kwammitin kula da Kin dadi alhaizan Alhaji Musa mallaha ya yabama Mai Daraja Governor zamfara Dr Dauda Lawan da ya aminta Kuma ya zabosu su shugaban ci maniyyatan Aikin hajji na wannan shekara ta 2023.
Ya Kuma Kara ya bama Mai Girma Gwamna bisa ga Dattijantaka da ya nuna a hukumar alhaizai ta jahar yace wasu jahohi du sun dakatar da mai'aikatan hukumar Amma anan yace tun da susuka tsara Aikin a barsu su tafi kasa Mai TSALKI.
Talban yace wajen Aikin zasu iyayinsu su tabbatar da bu nuna banbanci a lokacin Aikin hajji a kasa Mai TSALKI tsanin kowace jam'iyar siyasa fata anan agudanar da Hajj karbarbiya.
Shugaban kwammitin kula da Jin dadi alhaizan Alhaji Musa mallaha Talban Gusau Wanda yana tare da rakiyan membobinsa da suka hada da, Alhaji kasimu sani kaura, Hon yahaya Giwa maradun , Abubakar Bargaja Gummi, da Kuma sakatarensa Dr Aliyu Adamu (Bormo )Tsafe.
Comments
Post a Comment