Kungiyar Matasan ‘Yan Kasuwa taraba tallafi ga Magidanta 238 a Zamfara
Daga Aliyu Buhari Gusau
Shugaban kungiyar matasan yankasuwa na jihar Zamfara Alhaji Usman Isah samaila ya bayyana cewa kungiyar ta raba kayan agaji ga magidanta 238 a fadin jihar.
Alhaji Usman ya bayyana hakan ne jim kadan da kammala rabon kayan tallafin a Gusau babban birnin jihar. "Raba kayan agajin wani bangare ne na kokarin da kungiyar keyi na taimakawa mutane wajen rage radadi sakamakon cire tallafin manfetur, yayi kira ga wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace kadasu sayardasu.
“A cewar shugaban, kayayyakin da aka raba a matsayin tallafin, sun hada da shinkafa, spaghetti, indomie, macrony da sauran kayan abinci, yaci gaba da cewa ba shine karon farko da rabon kayayyakin abincinba” a wasu lokuta muna ba da tallafin abinci ga Almajirai 400 zuwa 1000 duk mako tsawon shekaru hudu da suka gabata a jihar”
Shugaban ’yan kasuwan ya kara da cewa, suna Samar da kudaden dasuke anfanidasu daga mambobinsu, yayi kira ga mambobin kungiyar dasu bawa shugabannin kungiyar goyon baya da hadin kai don samun ci gaba, ya kuma bada tabbacin zasu dauki kowa baidaya.
"Munakan shirye-shirye samar da magunguna don rabawa marassa lafiya a asibiti kyauta a fadin jihar"
Sakataren kungiyar matasan yankasuwa, kuma sakataren kungiyar halakan yankasuwa, Alhaji jamilu rabiu |
A jawabansu daban daban shugaban gamaiyan kungiyar yankasuwa Alhaji Muhammad zubairu da sakataren kungiyar matasan yankasuwa, kuma Sakataren hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwa, Jamilu Rabi’u, sunce dalilin raba wannan kayan abinci shine a taimaka wa al’ummar jihar, don rage musu radadin cere tallafin manfetur, sun yi kira ga masu hannu da shuni, kungiyoyin ‘yan kasuwa dasuyi koyi da da kungiyar wajen baiwa al’ummar jihar tallafi, sun shawarci al'umar jihar dasucigaba da addu'oin zaman lafiya dacigaban jihar, “Babu wata al’umma da zatacigaba batare da zaman lafiya ba” sun jaddada.
Comments
Post a Comment