Kungiyar Matasan yankasuwa ta bada tallafin Magunguna Kyauta ga Asibiti Mai zaman kanta a Zamfara.
Daga Aliyu Buhari Gusau
Kungiyar matasan ‘yan kasuwa ta jihar Zamfara ta bayar da tallafin magungunan da ya kai sama da naira dubu dari da hamsin (N150,000) ga asibitin Ashifa domin rabawa marassa galihu a jihar kyauta.
Ashifa Clinic wata cibiyar lafiya ce mai zaman kanta dake unguwar Firadakwaddi a cikin garin Gusau a jihar Zamfara.
Da yake mika magungunan ga shugaban asibitin Mallam Muhammad Kabir Muhammad wanda kuma shine mataimakin shugaban kungiyar likitocin musulmi ta kasa (IMAN) reshen jihar Zamfara, shugaban kungiyar matasan ‘yan kasuwa, Alhaji Usman Isah ya ce dalilin bayar da magungunan shine don taimakawa marayu. , mabukata da masu karamin karfi a jihar.
Alhaji usman ya bayyana cewa kungiyar za ta ci gaba da sawo magunguna domin rabawa ga asibitoci kyauta ga marassa galihu. "An sawo magungunan ne tare da tallafin membobin da ke ba da gudummawa akai-akai don tallafawa kungiyar”
A nasa gudunmuwar Sakataren kungiyar matasan ‘yan kasuwa Alhaji Jamilu Rabi’u, kuma sakataren hadin guiwar ‘yan kasuwa ya yabawa mahukuntan asibitin (IMAN) bisa gudun muwar dasukeyi ga asibitin, ya bukaci sauran likitocin da su yi koyi da irin taimakon da IMAN takeyi a jihar, Ya yi kira ga IMAN da ta yi amfani da magungunan cikin adalci sannan ya kuma ba da tabbacin bayar da duk wani tallafi da taimako ga asibitin idan bukatar hakan ta taso.
Alhaji jamilu rabiu, Ya yi kira ga gwamnatin jihar, ’yan siyasa, masu hannu da shuni dasu taimakawa asibitin Ashifa dake jihar.
Da yake mayar da martani, shugaban asibitin kuma mataimakin shugaban kungiyar IMAN Muhammad kabir Muhammad, ya godewa kungiyar matasan ‘yan kasuwa bisa wannan karamcin, ya kuma bukaci gwamnatin jiha da masu hannu da shuni da su yi koyi da kungiyar wajen ba da tallafin magungunan ga asibitoci, "Mu a matsayinmu na kungiyar likitocin Musulunci ta Najeriya mun yanke shawarar ziyartar asibitin a kowane mako domin kula da marasa lafiya tare da ba su magunguna kyauta, mun shafe sama da shekaru shidda muna yin haka ta hanyar gudunmawar da 'yan kungiyar suka bayar" IMAN ta jaddada.
Muhammad kabir Muhammad Ya bayyana hakan a matsayin ci gaban ga al'umar jahar, “Muna da likitoci daga asibitoci daban-daban wadanda suka hada da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, asibitin Yariman Bakura Specialist Hospital, Babbar Asibitin Gusau, Kin Fahad” Ya ce.
Comments
Post a Comment