Zamfara: Kungiyar masu sayar da waya ta Bebeji Plaza ta zabi sabbin shugabannin zartaswa.




Daga Aliyu Buhari Gusau 

Kungiyar masu sayarda wayoyi ta Bebeji plaza a jihar Zamfara sun zabi sabbin shugabannin dazasu gudanar da harkokin kungiyar na tsawon shekaru biyu a jihar.

Shugaban kwamitin zaben, Malan Mubarak Hassan ladan, ya ayyana Malan Hamisu Illiyasu a matsayin shugaban kungiyar,  mataimakin shugaban, Atiku Abubakar. Babban Imam, Zilfikali,  Ma'aji Surajo, Sakatare Abu maishinkafa, da Sadam Muhammad soja  a matsayin jami'in hulda da jama'a na 1, da sauransu.

A cewar Malan Mubarak Hassan ladan, mutane 15 ne suka fafata a mukamai daban-daban yayin zaben. 

Malan Mubarak ya bukaci sabbin shugabannin dasuji tsoron Allah, kuma sudauki dukkan mambobin kungiyar baidaya. 

Ya yabawa ’yan kungiyar bisa yadda suka fito a lokacin zaben, ya kuma bukacesu dasu bayarda hadinkai da goyon baya ga  sabbin zababbun shugabannin.

Ya yabawa muhimman mutanen  da suka halarci zaben, ya kuma yabawa jami’an tsaro bisaga samarda tsaro awajen zaben.

A jawabinsa na godiya, zababben shugaban kungiyar Malan Hamisu Illiyasu ya bayyana farin cikinsa da zaben, inda yabada tabbacin daukar kowa baidaya, 

"Na gamsu sosai da yadda aka gudanar da zaben, na kuma yabawa kwamitin zaben bisa gudanar da zabe makyau cikin aminci babu wata  fargaba.

"A shugabancina nayi alkwalin zansuminte filin Bebeji domin samun saukin kasuwanci, kasancewar alokacin damuna yankasuwa basuda walwala” shugaban yabba tabbacin  hakan.

Ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka wa kungiyar ta Bebeji domin samun ci gaba a jihar.

 "Kofota  koyaushe a bude take don ba da shawara, " in ji shugaban.

ya yabawa ’yan kungiyar bisa hadin kan da suke da shi, ya kuma yi kira garesu dasucigaba da hakan,  “duk wani dan kasuwa da ke zama a bebeji plaza to memba na ne, ba masu sayar da wayoyi kadai ba.

Comments

Popular posts from this blog

Permanent Secretaries' Forum Elects New Executives in Zamfara

Zamfara NSCDC Hosts Acting Provost FCET Gusau

Insecurity: Zamfara hospitals surfer brain drain - Doctor call rescue