An yi kira ga iyaye da maga'isa dasu horar da yayansu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada
Daga Suleiman Sani Danbarauka
An yi kira ga iyaye da maga'isa dasu horar da ‘ya’yansu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Shugaban makarantar Hizburrahim Talamizil Sheikh Ibrahim litahafizil Qur'an waddarasatul Islamiyya samaru Gusau Jahar Zamfara Alhaji Babangida mande (kwazon Gusau) ne yayi kiran a lokacin bukin yaye daliban makarantar yagudana aharabar makarantar.
Shugaban ya ce kiran ya zama wajibi bisa la'akari da cewa yara sune Manyan gobe.
Alhaji Babangida Ya bayyana ilimi a matsayin kashin bayan kowane ci gaba, yayi kira ga yara da matasa dasu nemi ilimin addinin Musulunci da na boko, ya kuma ba da tabbacin ci gaba da taimakawa makarantar idan bukatar haka ta taso, ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da masu hannu da shuni da su taimakawa makarantar domin bunkasa ilimin addinin musulunci a jihar.
Alhaji Babangida Ya taya daliban da suka kammala karatunsu murnar samun nasarar kammala karatunsu, ya kuma yi kira garesu da su zama jakadu nagari aduk inda sukasamu kansu.
A cikin wa'azin da suka gabatar awajen taron, Mallam Abdulhakim Ahmad yakub da mallam Nasir Assamrawi sun ruwaito cewa, Annabi (SAW) ya halatta wa kowane musulmi ya koyar da 'ya'yansa ya kyautatawa gareshi don yin alfahari dasu, dama wadanda suka kammala karatun Alkur'ani mai girma. (SWT) zaisakamasu da Aljanna mafi daukaka.
Tun da farko a jawabansu, Shugaban Makarantar Malan Hafiz Aliyu, da Mallam Balarabe, sun yi maraba da duk wadanda suka amsa gayyatarsu na halartar taron, inda suka yi addu’ar Allah ya mayar dasu gidaensu Lafiya, Sun kuma godewa duk wadanda suka bayar da gudumawa, a makarantar, sunyi addu’ar Allah ya saka masu da alheri.
Comments
Post a Comment