Gwamnatin Zamfara zata dauki matasa 250 aiki

Zamfara State Governor Dr,Dauda Lawal


Daga Aliyu Buhari Gusau

Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da daukar  matasa dari biyu da hamsin aiki  wadanda zasu yi aiki a matsayin jami’an kula da zirga-zirgar ababen hawa a jihar, ( ZAROTA) domin taimakawa wajen rage cunkoso da hadurran dake faruwa a wasu manyan tituna a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai mai dauke dasa hannun babban daraktan yada labarai da sadarwa. Mallan Nuhu Salihu Anka, yabaiwa jaridar gaskiya a Gusau babban birnin jihar.

A cewar Mallan Nuhu Salihu Anka, samar da ayyukan yi na nufin rage zaman kashe wando a tsakanin matasa a jihar, zai kuma taimaka wajen rage wahalhalun da tattalin arzikin da jihar ke fuskanta a halin yanzu da kuma kasa baki daya. 

“Wannan na daga cikin kudurin da aka cimma a zaman majalisar zartarwa na yau, wanda gwamna Dauda Lawal ya jagoranta, wanda aka gudanar a zauren majalisar, Gusau.

“Taron majalisar zartarwa wanda shine na goma sha shida, ya kuma umurci kwamishinan shari’a da kuma babban lauyan gwamnati dasu kafa kotun daza a bada alhakin kula da laifukan da suka shafi ababen hawa a jihar”

“Kazalika, taron ya amince da samar da wuraren shakatawa na tirela guda biyu domin rage cunkoson ababen hawa 

“A yayin ganawar, gwamna Lawal ya samu cikakkun rahotanni kan matsayin ayyuka daban-daban dake gudana wadanda suka shafi sassa daban-daban na jihar.

Taron ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar, Hon. Mani Malam Mummni, Sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Abubakar Nakwada, shugaban ma’aikata, Alhaji Mukhtar Lugga da daukacin ‘yan majalisar zartarwa na jiha.

Comments

Popular posts from this blog

Permanent Secretaries' Forum Elects New Executives in Zamfara

Zamfara NSCDC Hosts Acting Provost FCET Gusau

Insecurity: Zamfara hospitals surfer brain drain - Doctor call rescue