Kungiyar masu sayar da shayi da biredi ta yi kukan rufe gidajen biredi a Zamfara ---- Shugaban kungiyar
Daga Aliyu Buhari Gusau
Kungiyar masu sayar da shayi da biredi ta jihar Zamfara ta koka kan rufe gidajen biredin da kungiyar masu sayar da biredi ta yi a fadin kananan hukumomi 14 na jihar.
Shugaban kungiyar masu sayar da shayi da biredi na jiha, Alhaji Sani Magawata ya bayyana haka yayin wani taro da suka gudanar a makarantar firamare ta Danturai da ke Gusau babban birnin jihar.
Alhaji Sani Magawata yace manufar taron itace don hadin kansu, da kuma tattauna batutuwan da suka shafi kasuwancinsu.
"Muna kwana kusan 2 a gidajenmu saboda rashin yin burodin da za mu shirya sana'ar mu, don sana'armu daya bayayi saida daya” inji magawata.
Magawata ya bayyana alakar da ke tsakanin masu sayar da biredi da kungiyoyin masu sayar da shayi a matsayin mai kyau.
Magagawata ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta sa baki a kan lamarin, “muna da mambobi kusan 3000 kuma kasuwancin mu na yau da kullum ya gurgunta”
Ya yi kira ga ’yan kungiyar da su sabunta katin shaida zama Dan kungiya domin tsira da mutuncinsu.
A jawabansu na daban, sakataren kudi na jiha Alhaji Abdullahi Dodo da Alhaji Nasiru sun yabawa ‘ya’yan kungiyar bisa karrama wannan gayyata
Sun yi kira ga ’yan'yan kungiyar dasu kwantar da hankali da kuma bin doka da oda domin kungiyar na yin duk mai yiwuwa don ganin an daidaita lamarin.
Idan dai za a iya tunawa, kwanaki uku da suka gabata kungiyar masu sayar da biredi ta jihar Zamfara ta sanar da dakatar da yin biredi a fadin jihar nan ba da dadewa ba ga abin da suka bayyana tsadar kayan biredi.
Comments
Post a Comment