Dan takarar Shugabancin kananan hukumomi na PDP ya tsallake rijiya da baya a Zamfara
![]() |
Hon Umar A Faru (Customs) |
Daga Bello Hashim Bungudu
Dan takarar shugabancin karamar hukumar Bukkuyum Hon Umar A Faru (Customs) ya tsallake rijiya da baya.
Hon Umar A Faru ya bayyana haka ne jim kadan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP da aka gudanar a garin Bukkuyum.
Hon Umar Faru ya zargi Kantoman karamar hukumar Bukkuyum Hon Nasiru Muhammad DG da daukar hayar yanta'adda daga Zuru, Sokoto da Riba domin su halaka shi.
"Jama'ar da nake dasu a Bukkuyum shinassa Hon Nasiru Muhammad DG yake kyashi, shi yassa ya dauki wani mummunan mataki ya cutar da ni, ya bayyana hakan a matsayin babban abin takaici" A Faru yabayyana hakan.
Comments
Post a Comment