"Ni ne sahihin shugaban kungiyar 'yan kasuwa na jihar Zamfara"--- Inji Maikanwa
Daga Shamsu Idris Gusau
Alhaji Ibrahim Sani Maikanwa ya ce babbar kotun tarayya dake Gusau ta tabbatar dashi a matsayin sahihihin shugaban kungiyar ‘yan kasuwan jihar Zamfara.
Alhaji Ibrahim Sani Maikanwa ya bayyana hakan a Gusau babban birnin jihar, ya ce a ranar Litinin Babbar kotun tarayya dake Gusau ta amince dashi a matsayin sahihin shugaban Kungiyar, ya kuma gargadi duk wani Mutum dake bayyana kansa a matsayin shugaban kungiyar daya daina yada labaran karya.
Alhaji Ibrahim Sani Maikanwa ya bada tabbacin farfado da kungiyar yan kasuwan jihar Zamfara
“Ina da shirye-shiryen kafa Kamfanoni a dukkan kananan hukumomi 14 domin al'ummar jihar su kasance masu dogaro da kai, musamman irin wannan yanayi damuke ciki a yanzu," in ji Makanwa.
"Zan gyara harkokin kasuwanci a jihar" Maikanwa ya tabbatar.
"Mun zagaya zuwa wasu kasashe, don Samo wasu hanyoyi dammukafa kamfanona don cigaban jiharmu” inji Maikanwa.
Maikanwa ya godewa Allah da ya tabbatar dashi amatsayin sahihin Shugaban Kungiyar yankasuwa, ya kuma bada tabbacin yin adalci ashugabancinshi, yayi kiraga yayan kungiyar dasu maramashi baya don cimma nasara.
Maikanwa yayi kiraga yankasuwa da mutanen jihar dasu bashi hadinkai da goyon baya doncimma nasara.
“Kofata abudetake don ansar shawara, ko korafi daga yayan kugiya” inji Maikanwa.
Comments
Post a Comment