Tsohon dan majalisar tarayya ya bukaci gwamna Dauda Lawal da yasa baki kan batun tsige shugabannin PDP a Zamfara

Hon. Kabiru Yahaya Classic

Daga Bello Hashimu Bungudu 

Tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Anka da Mafara Hon. Kabiru Yahaya Classic ya bukaci gwamnan Dauda Lawal da yasa baki kan batun tsige wasu shugabannin PDP na karamar hukumar Mafara a jihar Zamfara.

Hon. Kabiru Yahaya Classic yayi wannan kiran ne a wata ganawa da ya yi da shugaban karamar hukumar Mafara na PDP da wasu Shugabanni da Magoya bayan jam’iyyar da aka gudanar a Mafara. 

Hon Kabiru ya bayyana cin zarafi da cin mutunci da wasu jiga-jigan jam'iyyar suka yi masa a yankin Mafara amatsayin abuntakaici,"Duk da cewa PDP Iyali daya ce amma wasu na amfani da sha'awarsu wajen ruguza jam'iyyar" inji Classic. 

Ya yabawa magoya bayan jam’iyyar kan yadda suka fito, ya kuma yi kira garesu dasu cigaba da marawa Gov. Dauda lawal baya domin samun Nasara. Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar dasu cigaba da addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Comments

Popular posts from this blog

Permanent Secretaries' Forum Elects New Executives in Zamfara

Zamfara NSCDC Hosts Acting Provost FCET Gusau

Insecurity: Zamfara hospitals surfer brain drain - Doctor call rescue