Danmajalisar Taraya a jahar zamfara Mai wakilta kaura da Birnin magaji ya Samar da santoci 41 na Abincin Azumi ga Marayu da marasa galihu har karshen watan Ramadan.


From: Haruna Muhd Gusau.

Danmajalisar Taraya a jahar zamfara Mai wakilta kaura Namoda da Birnin magaji Hon. Aminu Sani jaji ya Samar da santoci 41 na Abincin na Buda Bakin ga Marayu da marasa galihu a fadin jahar zamfara.

Dayake bayani wajen kaddamar da Talafin Abincin Danmajalisar Taraya Hon. Aminu Sani jaji ya samu wakilta state coordinator nashi waton Hon. Aliyu Abubakar MC Tsare, a wajen kaddamar da Talafin a garin Gusau.

Acewar wakilin Danmajalisar Taraya Hon Aliyu Abubakar MC Tsafe,yace kamar dai yadda aka saba du Shekara Danmajalisar Taraya Yana gudanar wannan Talafi zuwa ga marayu da marasa galihu domin buta Bakin Azumi, bana ma ankara Abincin la'akari da yawaitar mabukata a cikin al'umma.

Wannan ciyar dai za'a gudanar da ita a dukanin local government goma 14 da ke jahar zamfara tun daga farkin Azumi har Zuwa karshen watan Ramadan fissabilalah.

Hon. Aliyu Abubakar MC Tsafe, yace committee Mai karfin gaske a ka nada domin kula da wannan ciyarwa a dukanin fadin jahar zamfara.

Ya Kara dacewa dukkan nin santocin Nan 41 za'a ziyartarsu daya bayan daya  ga wannan committee da'a aka nada Wanda malam Atiku sani Maradun sa'in zamfara ke jagoranta.

Hon. Aliyu Abubakar MC Tsafe yayi Kira ga wafdanda aka Hannun tawa wannan ciyarwa dasu ji tsoron Allah su kamata gaskiya da adalci wajen gudanar da wannan ciyarwa a ko Ina fadin jahar zamfara.

Har wayau a wajen Taron shugaban committee da aka nada domin ziyar tar yadda ciyarwar zata gudana Malan Atiku sani Maradun sa'in zamfara yace committee Yana dauke da membobinsa zasu Guda nar da Aikin su cikin adalci da gaskiya kowa ce Santa sai su ziyarta a fadin 14 local government dake zamfara don ganin ma idonsu a bunda ke gudana.

Malam Atiku sani Maradun sa'in zamfara yace dukanin abunda masu dafa wannan abinci ke bukata an basu tare Kara masu ihisani Mai soka don attabatar da an gudanar da adalci wajen gudanar da wannan ciyarwa ta wannan wata Mai albarka.Saboda haka Babu wani dalili da zai ka kasa yin gaskiya wajen wannan aiki idon muka kama akasin haka to doka zatayi aikinta.

Ya Kuma godewa Danmajalisar Taraya Hon.Aminu Sani jaji bisa wannan Aikin alheri da yake yi dukkan Azumi watan Ramadan fissabilalah.

Comments

Popular posts from this blog

Permanent Secretaries' Forum Elects New Executives in Zamfara

Zamfara NSCDC Hosts Acting Provost FCET Gusau

Insecurity: Zamfara hospitals surfer brain drain - Doctor call rescue