CIBIYÂR KASUWANCI TA JIHAR ZAMFARA NA YIWA MAIGIRMA GWAMNA DAUDA LAWAL BARKA DA BABBAR SALLAH
![]() |
| President Zamfara State Chamber of Comerce Mines and Agriculture, Dr, Hasan Buhari Tafida |
Ni Dr. Hassan Buhari (Tafidan Maradun), Shugaban cibiyar Yankasuwar Jihar Zamfara, a madadi na da duk mambobin wannan cibiya, inar da sakon murna na Babbar Sallah zuwa maidaraja Gwamna Dauda Lawal.
Muna kuma isar da murnár mu ga manyan mutane da mukarraban gwamnati bisa wannan lokaci da Allah Ya nuna muna, na Babbar Sallah.
Muna jijina wa maidaraja Gwamna bisa kokarin ka wajen kawar rashin tsaro da fata gari a duk fadin Zamfara. Allah taimake ka wajen hubbasa domin kawo zaman lafiya da tsaro a Zamfara.
Allah Ya baka lafiya domin ganin bádin badada, da muma zimmar ciyar da Zamfara a gaba.
Barka Da Sallah
Daga:
Dr. Hassan Buhari Tafida,
Shugaban ZACCIMA.

Comments
Post a Comment