Ubankasar Gada Biyu ya tabbatar da sabon Jekadan Gada Biyu
From Ishaka Muhammad Tukur
Ubankasar Gada Biyu, Alhaji Jamilu Muhammad Kabiru Danbaba, ya tabbatar da nadin Maigirma Ishaka Muhammad Tukur MD (Dankullum TV) a matsayin Jekadan Gada Biyu.
Takardar tabbatarwar, wadda aka fitar a ranar Laraba 24 ga Disamba, 2025, ta nuna cewa an ba shi wannan sarauta ne bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen cigaban yankin Gada Biyu da al’ummar yankin baki É—aya.
A cikin takardar, Ubankasar Gada Biyu ya bayyana fatan sabon Jekadan zai ci gaba da bada gudunmawa wajen ci gaban yankin da kuma tallafa wa harkokin al’umma.
Har ila yau, an yi masa fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya ba shi ikon rike wannan sarauta da kuma tsawaita zamaninsa a kan mukamin.

Comments
Post a Comment