FRSC ta horar da ZAROTA kan harkokin zirga-zirgar ababen hawa tare da yimasu gargadi game da cin zarafin jama'a a Zamfara



Daga Aliyu Buhari Gusau 

Hukumar Kula da Tsaron Hanya ta Tarayya (FRSC) ta gudanar da horo ga hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Zamfara (ZAROTA) kan harkokin zirga-zirga, tare da yimasu gargadi game da cin zarafin jama'a a jihar.

An gudanar da horon ne a zauren taro na kungiyar NURTW da ke kan hanyar 'Bye-pass' a Gusau, babban birnin jihar. 

Kwamandan hukumar FRSC na jihar, Aliyu Ma'aji, ya bayyana cewa an shirya horon ne domin fadakar da jami'an ZAROTA kan dokoki da ka'idojin da ke tafiyar da harkokin zirga-zirgar ababen hawa. 

Aliyu Ma'aji ya jaddada cewa, ba a yarda jami'an ZAROTA su rika tsoratarwa, kunyatawa, ko bata sunan kowa ba. Ya kuma yaba wa Kwamandan ZAROTA bisa kokarinsa na inganta harkokin hukumar. 

A nasa jawabin, Kwamandan ZAROTA, Muhammad Bello Musa, ya yabawa 'yan sanda, hukumar Civil Defence, da kuma DSS bisa goyon bayan da suke bai wa ZAROTA. 

Ya bayyana cewa akwai kararrakin da suka shafi ZAROTA guda 48 a kotu, inda ya ce, "Mutane da dama sun tuntube ni cewa jami'an ZAROTA suna kunyata su, lamarin da bai dace ba." Yayaba wa FRSC bisa wannan horo, tare da yin kira ga jami'an ZAROTA su yi amfani da abin da suka koya a yayin horon.

 A nasa jawabin, Sarkin Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello wanda Hakimin Tudun Wada, Alhaji Nuraddeen Kabir Dan Baba, ya wakilta, ya bayyana farin cikinsa game da horon tare da yaba wa FRSC.

A jawabansu daban-daban, wakilan 'yan sanda, Civil Defence, da DSS sun yaba wa FRSC bisa horon, tare da bayyana cikakken goyon bayansu da hadin kai.

Comments

Popular posts from this blog

About 9 People dead in a auto crash in Zamfara ---- FRSC

New Leadership of the Chairmen's Forum of NYCN Has Emerged

FMC Gusau re-affirms Commitment towards upgrading to a teaching hospital