MATSALAR KARANCIN RUWAN GUSAU ZATA ZAMA TARIHI - ENG BUHARI SALISU DOSARA MD ZAMFARA WATER BOARD

Eng Buhari Salihu Dosara FROM HARUNA MUHD GUSAU An yi Kira ga alummar cikin garin Gusau da kewaye dasu Kara hakuri dangane da matsalar karancin ruwan Sha da ta addabe su. Wannan Kiran ya fitone daga bakin shugaban hukumar bada Ruwansha ta Zamfara, Eng Buhari Salihu Dosara a lokacin da yake ganawa da manema labaru a ofishinsa. Eng Buhari Salihu Dosara yace matsala ta faru ne sanadiyar karanci wutar lantarki dake addabar jahar musamman babban birnin jahar. Ya Kuma ba al-ummar jahar hakuri in sha Allah injiniyoyinsu suna nan su na bakin kokarin don tabbatar da cewa matsalar tazamo tarihi a cikin jihar baki daya. Ya Kuma Kara da cewa ma'aikatan gidan ruwa suna iya yin su domin tabbatar da cewa ruwan Sha sun yawaita 24 hour ga al-ummar jahar Amma saboda wasu matsalolin musamman abin da ya shafi na urorin bada ruwan Shan akasarin sun jima suna Aiki fiye da shekaru 30 ana amfani dasu. Manajan Wanda yayi fatan alheri ga Mai Daraja zabbaben Gwamnan...